Sifeto Janar din Najeriya ya janye jami'an dake baiwa fitattun mutane tsaro

Sifeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya Muhammadu Adamu ya bada umurnin janye jami’an sa dake kula da lafiyar wasu fitattun mutane da kungiyoyi a fadin kasar.

Wasu 'Yan Sandan Najeriya a Legas
Wasu 'Yan Sandan Najeriya a Legas AFP / Pius Utomi Ekpei
Talla

Sanarwar da rundunar Yan Sandan ta bayar ta bayyana wadanda umurnin ya shafa da suka hada da tsoffin ministoci da tsoffin sakatarorin Gwamnati da jiga-jigan ‘yan kasuwa.

Sauran sun hada da shugabannin addinai da kuma yan kasuwa wadanda aka baiwa umurnin komawa ofishin su cikin gaggawa.

Matakin Sifeton ‘Yan Sandan Najeriyar na zuwa ne bayan shelar soma yiwa rundunar jami’an tsaron garambawul da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sanar a dalilin zanga-zangar kin jinin cin zalin da wasu ‘Yan Sandan rundunar SARS ke yi, da matasa suka yi a sassan Najeriya, zanga-zangar da daga bisani ta rikide zuwa tarzoma.

Akalla mutane 40 ne rahotanni suka tabbatar da mutuwarsu, tare da asarar tarin dukiya, dalilin rikicin da ya biyo bayan zanga-zangar ta EndSARS da ta shafe makawanni 2 tana gudana musamman a jihar Legas da wasu jihohin kudancin Najeriya ciki har da Osun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI