Najeriya

Fiye da kashi 14 na 'yan Najeriya na shan wiwi

Gwamnatin Najeriya ta ce kusan kashi 14 da rabi na al’ummar kasar na shan wiwi ko hodar ibilis ko kuma kodin da ke tagayyara hankalinsu.

Yadda wasu ke mola wiwi
Yadda wasu ke mola wiwi REUTERS/Jorge Dan Lopez
Talla

Daraktar da ke Yaki da Masu Amfani da Haramtattun Kwayoyi a Hukumar NDLEA Titus-Awogbuyi Joyce ta sanar da haka sakamakon alkaluman da hukumar ta tattara a shekarar 2018.

Jami’ar ta ce, alkaluman sun kuma bayyana cewar, daga cikin mutane 4 da ke ta'ammuli da wadannan miyagun kwayoyi guda mace ce, abin da ke nuna yadda matsalar ta shafi kowanne bangare.

Hukumar Yaki da Amfani da Miyagun Kwayoyin na Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane miliyan 246 suka yi amfani da irin wadannan kwayoyi a duniya daga shekarar 2014.

Ministan Kasafin Kudin Najeriya da Tsare-Tsare, Prince Clem Ikanade Agba ya ce matsalar na yi wa kasa matukar illa wajen ci gabanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI