Dangote ya musanta samun fifiko daga gwamnati wajen fitar da kaya
Hamshakin Attajirin Afrika dan Najeriya Aliko Dangote ya yi watsi da rahotan cewar gwamnatin Najeriya ta bashi damar fitar da siminti zuwa kasashen waje a daidai lokacin da ta rufe iyakokin ta, matakin da ya haifar da zazzafar mahawara a cikin kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Alhaji Aliko Dangote na mayar da martani ne sakamakon korafe korafen da suka mamaye Najeriya cewar gwamnatin kasar ta bashi damar fitar da simintin da kamfanin sa ke sarrafawa zuwa kasashen Nijar da Togo, yayin da aka hana sauran kamfanoni saboda rufe iyakar da akayi.
Shugaban kamfanin simintin Dangote Michel Pucheos ya bayyana damar da suke da ita lokacin da yake jawabi ga masu zuba jari a Lagos, inda yace gwamnatin Najeriya ta basu wannan dama.
Wannan labari ya harzuka Yan kasuwa da kamfanoni da dama wadanda ke tambaya akan dalilin da ya sa gwamnatin kasar ta fifita kamfanin Dangoten wajen bashi wannan dama tun daga watan Yulin bana.
Shugaban Bankin IBTC Atedo Peterside ya bayyana damuwa kan yadda gwamnati ta fifita Dangote a maimakon sauran kamfanonin kasar.
Sai dai Babban jami’in sadarwar kamfanonin Dangote, Anthony Chiejina yayi watsi da labarin, wanda ya bayyana shi a matsayin labarin kanzon kurege.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu