Najeriya

Tsohon gwamnan Kaduna Balarabe Musa ya rasu

Marigayi Abdulkadir Balarabe Musa
Marigayi Abdulkadir Balarabe Musa DailyPost

Tsohon gwamnan jihar Kaduna ta Najeriya, Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya rasu yana da shekaru 84 a gidansa da ke birnin Kaduna bayan ya yi fama da jinya.

Talla

Wakilinmu Aminu Sani Sado da yanzu haka ke gidan marigayin, ya shaida mana cewa, za a gudanar da jana’izarsa da misalin karfe 4 na yammacin Larabar nan a Masallacin Sultan Bello.

Sanata Shehu Sani wanda abokin huldar siyasar marigayin ne, ya tabbatar da rasuwarsa a shafinsa na Twitter a safiyar ranar Laraba.

Yanzu haka manyan 'yan siyasa da suka hada da kwamishinoni na ci gaba da tururuwa zuwa gidan marigayin kamar yadda wakilinmu ya tabbatar mana.

A shekarar 1979 ne aka zabi Balarabe Musa a matsayin gwamnan jihar Kaduna, amma daga bisani an tsige shi daga karagar mulki.

Ana kallon Musa a matsayin dan siyasa mai rajin tabbatar da ci gaba, yayin da ya sha sanya kafar wando daya da mulkin soji a zamanin Sani Abacha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.