Covid-19: Najeriya za ta karbi bashin dala miliyan 750

Ministar kudin Najeriya Zainab Ahmed, ta ce gwamnatin tarayyar kasar na shirye-shiryen karbar bashin dala miliyan 750 daga bankin duniya, domin rage tasirin radadin da annobar coronavirus ta haifar ga tattalin arzikin kasar.

Dalar Amurka
Dalar Amurka REUTERS/Jose Luis Gonzalez/File Photo
Talla

Minister kudin Najeriyar ta bayyana haka ne a Abuja, yayin kaddamar da wasu kwamitocin farfado da tattalin arzikin kasar daga shakar mutuwar da annobar ta Covid ta yi masa.

Zainab Ahmed ta ce gwamnatin Najeriya za ta aiwatar da shirin farfado da tattalin arzikin ne ta hanyar rabawa gwamnatocin jihohi bashin da take shirin karbowa daga bakin duniya na dalar Amurka dubu 750.

Kamar sauran kasashen duniya musamman masu tasowa a nahiyar Afrika, annobar coronavirus ta yi mummunan tasiri wajen nakasa tattalin arzikin Najeriya, sakamakon tilasatawa hukumomin kasar hana zirga-zirga da kuma killace miliyaoyin mutane a gidajensu, matakan da suka gurgunta kasuwanni da sauran sana’o’in hannu, baya ga kamfanoni da sauran ma’aikatu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI