Najeriya

Gwamnatin Najeriya na shan caccaka kan karin farashin litar mai

Sabuwar matatar man da hamshakin attajirin Najeriya da ma Afrika Aliko Dangote ke ginawa a Ibeju dake unguwar Lekki a jihar Legas. 5/7/2018.
Sabuwar matatar man da hamshakin attajirin Najeriya da ma Afrika Aliko Dangote ke ginawa a Ibeju dake unguwar Lekki a jihar Legas. 5/7/2018. REUTERS/Akintunde Akinleye/File Photo

'Yan Najeriya na cigaba da bayyana ra'ayoyinsu kan karin farashin litar man fetur daga naira 160 zuwa naira 171, sakamakon kwaskwarimar da hukumar kayyade frashin albrkatun man na fetur ta kasar ta yi wa farashin man daga inda ake dakonsa, inda yanzu litar ta tashi daga naira 147.87 zuwa N155.17.

Talla

Rahotanni sun ce tuni wasu gidajen saida man suka soma kara farashin litarsu zuwa naira 170.

A jiya Juma'a 13 ga watan Nuwamba ne kuma kungiyar masu sana’o’in hannu ta Najeriya ta bi sahun masu caccakar karin farashin litar man, inda ta bayyana manufofin gwamnatin kasar kan tattalin arziki da cewar suna yiwa ‘yan Najeriya illa fiye da annobar coronavirus wajen kara jefa talakawa cikin kunci.

Yayin taron manema labarai a Abuja, babban sakataren kungiyar masu sana’o’in ta Najeriya Komolafe Gbenga ya zargi gwamnati da gazawa wajen cika alkawuran gayara matatun man kasar, don kawo karshen shigo da tataccen man daga kasashen ketare, abinda ke taka rawa wajen hauhawar farashinsa babu kakkautawa.

Gwamnatin Najeriyardai na cigaba da kare manufofinta na janye baki dayan tallafin da take baiwa fannin sassauta farashin man a watannin da suka gabata, inda tace kasuwar man ce zata rika fayyace farashin da za a rika saida litarsa a kasar. Matakin da tace ya zama dole la’akari dafaduwar farashin gangar danyen man a duniya, abinda ya haifar da koma baya ga tattalin arzikin Najeriyar.

Sai dai yayin zantawa da sashin Hausa na RFI, Farfesa Muntaka Usman na Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria masanin tattalin arziki, ya dora alhakin hauhawar farashin litar man a Najeriya kan tasirin basukan da gwamnatin kasar ke karba daga hukumomin kasada kasa, wadanda Farfesan yace su ke tsara wasu manuofin tattalin arzikin da ke kuntatawa talakawa.

Farfesa Muntaka Usman na Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria masanin tattalin arziki kan karin farashin litar mai a Najeriya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.