Najeriya: Cutar Pneumonia na halaka kananan yara dubu 140 duk shekara
Ma’aikatar lafiyar Najeriya ta fitar da sabbin alkaluman da suka nuna cewa cutar Pneumonia na kashe kimanin yara ‘yan kasa da shekaru 5 dubu 140 duk shekara a kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Rahoton ya ce lamarin ya kara muni ne saboda yadda annobar coronavirus ta dakile damar da a baya kananan yaran masu fama da cutar ta Pneumonia ke samu na amfanin da na’urorin taimaka musu wajen yin numfashi da suka hada da na’urar shakar iskar Oxygen da wasu magunguna ajin antibiotics, wadanda a yanzu hukumomin lafiya suka karkatar da su ga masu fama da cutar coronavirus.
A ranar Alhamis 12 ga watan Nuwamban da muke aka yi bikin ranar wayar da kai dangane da Pneumonia a duniya, cutar da karamin ministan lafiyar Najeriya Oloruninimbe Mamora yace tana halaka jarirai akalla 132 daga cikin dubu 1 da ake haihuwa duk shekara a kasar.
Kwayoyin cuta na bacteria ko virus ne ke haddasa cutar Pneumonia wadda ke yiwa yara illa ta hanyar toshe musu huhu, abinda ke kassara samun numfashi.
Baya ga haifar da cikas ga shirin yaki da cutar Pneumonia, annobar coronavirus ta haifar da nakasu ga wasu karin shirin baiwa kananan yara kulawa a Najeriya da suka hada da yi musu alluran rigakafin cutuka daban daban, da samun tallafin abinci mai gina jiki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu