Najeriya

Kusoshin APC sun amince da gazawar Buhari kan tsaro

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. © Nigeria Presidency

Wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya sun jingine batun siyasa a gefe, inda suka amince cewa, gwamnatin Muhammadu Buhari ta gaza  samar da tsaro, ganin yadda 'yan bindiga ke garkuwa da jama'a hatta akan hanyar Abuja, babban birnin kasar.

Talla

A yayin zantawarsa da Sashen Hausa na RFI, Hon. Muhammed Umaru Bago, dan majalisar wakilai daga jihar Niger kuma jigo a jam'iyyar APC, ya bayyana cewa, ko dai shugaba Buhari ya rasa masu fada masa gaskiya ko kuma ya yi kunnen kashi.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirarsa da Muhammad Sani Abubakar.

Kusoshin APC sun amince da gazawar Buhari kan tsaro

Hon. Bago ya bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki matakin share dazukan da 'yan bindiga ke buya a cikinsu domin ci gaba da aiwatar da miyagun ayyukansu a sirce.

Ya kamata Najeriya ta jingine duk wani aikin kwangila a halin yanzu domin karkata kudaden wajen yaki da matsalar tsaro a cewar dan majalisar.

Ba kasafai ake samun mambobin jam'iyya mai mulki ba da ke fitowa karara suna bayyana rashin jin dadinsu kan gazawar gwamnatinsu a Najeriya, ganin yadda akasarinsu ke rufa-rufa da sunan kare martabar jam'iyyar.

Sai dai Hon. Bago ya bayyana cewa, rayukan 'yan Najeriya sun fi muhimmanci fiye da siyasa.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.