Bakonmu a Yau

Jami'an tsaro basu kashe kowa a Lekki ba - Buhari

Wallafawa ranar:

A karon farko gwamnatin Najeriya ta ce babu ko da mutum guda da jami`an tsaro suka kashe a shingen karbar harajin ababen hawa a hanyar Lekki da ke Legas, a lokacin zanga-zangar EndSARS.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin ganawa da mataimakin shugaban Majalisar kasar
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin ganawa da mataimakin shugaban Majalisar kasar © Nigeria Presidency
Talla

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya musanta zarginda ake yiwa sojan kasar cewa sun kashe masu zanga-zangan ENDSARS a kwanan baya.

Shugaban yace, bayanan da aka yi ta yadawa ta kafafen sada zumunta jita-jita ne kawai, babu gaskiya a ciki.

Masu zanga-zangar da wasu kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun yi zargin cewa an kashe a kalla mutane 12 a harabar ta Lekki.

Kan haka ne muka tattauna da Malam Garba Shehu, kakakin shugaban kasa Mohammadu Buhari, kuma ga abinda yake cewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi