Atiku ya bukaci karawa attajirai haraji don farfado da tattalin arzikin Najeriya
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma tsohon dan takarar shugaban kasar karkashin jam'iyyar adawa PDP, Atiku Abubakar, ya baiwa gwamnatin Najeriya shawarwari don fita daga cikin kangin talauci da kasar ta shiga.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Cikin shawarawari da Atikun ya baiwa gwamnatin Najeriyar, harda bukatar karawa attajirai haraji.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma nuna bacin rai sakamakon yadda Najeriya ta kara shiga halin karayar tattalin arziki, inda ya zargi gwamnatin Buhari da kin amincewa da shawarwari da ya yi ta basu.
A ranar Asabar ne dai Hukumar kididdiga ta Najeriya ta ce tattalin arzikin kasar ya ragu da kashi 3.62 cikin 100 a tsakanin watan Yuli zuwa Satumban 2020, wanda hakan ke nufin tattalin arziƙin ƙasar ya samu karaya.
Hukumar ta dora alhakin haka a kan faduwar farashin danyen mai a kasuwannin duniya da kuma tasirin annobar coronavirus.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu