Sojoji aka kaiwa hari ba Zulum ba - Gwamnatin Borno
Gwamnatin Jihar Barno ta musanta rahotanni da ke cewa mayakan Borko Haram sun kai hari kan ayarin motocin gwamnan jihar Farfesa Babagana Umara Zulum.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Sanarwar da kakakin gwamnatin jihar Malam Isa Gusau ya fitar na cewa gwamna Zulum ya kai ziyara garin Baga, inda ya raba kayan abinci ya kwana guda a can, kuma ya dawo gida cikin koshin lafiya, babu wani hari da aka kai masa ko tawagar ‘yan rakiyarsa.
Sai dai rahotanni sun tabbatar da wani harin da ya hallaka akalla Sojojin Najeriya 7 da matashin Civilian JTF guda, a wani harin kwantar bauna da mayakan Boko Haram dake da alakada Kungiyar ISIS suka kaiwa ayarin motocinsu a kauyen kwayamti kusa da Maiduguri.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu