Najeriya

Kotu ta aike da Ali Ndume gidan yari kan gaza gabatar da Maina

Sanata Ali Ndume.
Sanata Ali Ndume. RFI Hausa

Wata Kotu a Najeriya ta bada umurnin tasa keyar sanata Ali Ndume gidan yarin Abuja saboda gazawa wajen gabatar da Abdurasheed Maina, tsohon shugaban kwamitin fanshon da ya karbi belin sa a gaban kotun.

Talla

Maina na fuskantar tuhumar almundahanar da ta shafi naira biliyan 2 ne daga asusun ajiyar fanshon ma’aikatar, abinda ya sa ya gabatar da Sanata Ndume a matsayin wanda ya karbi belin sa.

Mai shari’a Okong Abang ya bada umarnin kai Sanatan gidan yarin Kuje da kuma raba shi da gidan sa da ya gabatar a matsayin jinginar belin akan kudin da ya kai naira miliyan 500.

Shi dai Ndume ya shaidawa kotun cewar ya gabatar da kan sa a matsayin wanda ya karbi belin Maina ne saboda alkalin kotun ya bukaci wanda ake zargi ya gabatar da mai rike da mukamin sanata, kuma wanda zai dinga gurfana a gaban kotun duk lokacin da ake gudanar da shari’ar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.