Najeriya

'Yan bindiga sun sace malami a Jami'ar Ahmadu Bello

Satar Mutane don neman kudin fansa ya zama ruwan dare a Najeriya mai fama da rikici.
Satar Mutane don neman kudin fansa ya zama ruwan dare a Najeriya mai fama da rikici. REUTERS/Goran Tomasevic/File Photo

Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a Najeriya ta sanar da cewar wasu 'yan bindiga sun kutsa kai cikin harabar ta inda suka dauke wani malami da matar sa da kuma ‘yar sa guda, kwana guda bayan sakin wasu dalibai 9 da aka yi garkuwa da su.

Talla

Daraktan yada labaran makarantar Auwalu Umar ya ce an sace malamin ne a ‘Sardauna Crescent’ da ke cikin makarantar a Samaru, yayinda lokacin da jami’an tsaro suka bisu, sai suka saki matar malamin da diyar sa.

Matsalar satar mutane ana garkuwa da su a sassan arewacin Najeriya na neman zama ruwan dare, ganin yadda ake dibar matafiya da mutane a Masallatai da wasu a gidajen su.

Rahotanni sun ce sau tari sai ‘yan uwan wadanda aka sace sun sayar da kadarorin su kafin kubutar da su, yayin da a wani karo ma koda an biya ba’a sakin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.