Najeriya

Buhari ka ji tsoron Allah ka cika alkawarinka-ACF

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. businessday

Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta ACF ta ce, matsalar tsaro ta tsananta a arewacin Najeriya, tana mai kira ga shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya ji tsoron Allah, sannan ya cika alkawuran da ya yi wa ‘yan kasar na samar da zaman lafiya.

Talla

Kungiyar ta bayyana cewa, shugaba Buhari ya fi kowa sanin laifin da ke tattare da rantsuwa da al-Kur’ani mai girma ba tare da cikawa ba.

ACF ta ce, ta damu matuka kan yadda ‘yan bindiga ke ci gaba da kashe al’umma a yankin arewacin Najeriya duk da ikirarin Ministan Kula da Ayyukan ‘Yan sanda da ke cewa, an ci galabar ‘yan bindigan.

A cikin sanarwar da ta fitar, ACF ta ce, tana wakiltar dimbin al’ummar arewacin Najeriya wajen isar da fushinsu ga shugaba Buhari da zummar ganin ya gaggauta daukar mataki.

ACF ta yi tur da sabbin hare-haren da ‘yan bindiga suka kaddamar kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja da kuma sace daliban Jami’ar Ahmadu Bello su tara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.