Najeriya

Sojojin Najeriya sun yi luguden wuta kan 'yan ta'addan Borno

Sojin saman Najeriya sun yi wa 'yan ta'adda luguden wuta a tungarsu da ke kusa da Tafkin Chadi.
Sojin saman Najeriya sun yi wa 'yan ta'adda luguden wuta a tungarsu da ke kusa da Tafkin Chadi. DailyPost

Rundunar sojin saman Najeriya ta Operation Lafiya Dole ta kashe tarin ‘yan ta’adda a wani harin sama da ta kaddamar musu a tungarsu da ke kusa da yankin Tafkin Chadi a jihar Borno.

Talla

Jami’in Yada Labaran Rundunar Manjo Janar John Eneche ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a birnin Abuja.

Manjo Eneche ya ce, a ranar 22 ga wannan wata na Nuwamba aka kaddamar da farmakin bayan wasu bayanan sirri sun bankado wurin da ‘yan ta’addan na mayakan IS reshen Yammacin Afrika ke buya.

Sanarwar ta kara da cewa, tungar ‘yan ta’addan na dauke da rumfunan wucen-gadi masu launin kakin sojoji , yayin da suke amfani da wannan tunga wajen safarar kayayyaki zuwa wasu wurare daban daban a kusa da tafkin Chadi.

Rundunar sojin ta Najeriya ta yi amfani da jiragen yaki da jirage masu saukar ungulu wajen luguden wuta kan ‘yan ta’addan masu ikirarin jihadi

Rundunar ta kuma yi nasarar raba mayakan da makamansu kamar yadda Manjo Eneche ya bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.