Najeriya-Lafiya

Cutar Kanjamau ta hallaka 'yan Najeriya dubu 45 a 2019- MDD

Babbar Jami'ar hukumar ta ce adadin abin fargaba ne kan halin da masu cutar ke ciki a Najeriya.
Babbar Jami'ar hukumar ta ce adadin abin fargaba ne kan halin da masu cutar ke ciki a Najeriya. Jekesai NJIKIZANA / AFP

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke yaki da cutar kanjamau ta bayyaan cewar akalla 'yan Najeriya 45,000 da ke dauke da cutar suka mutu a shekarar 2019, abinda ke bayyana fargaba daga masu fama da ita.

Talla

Fiona Braka, jami’ar Majalisar ta bayyana haka ga manema labarai gabanin gudanar da bikin ranar yaki da cutar na wannan shekarar.

Braka ta ce wannan ba abu ne da za a lamunce da shi ba, a dai dai lokacin da gwamnatoci da kungiyoyin agaji da jama’a ke bada gagarumar gudumawa domin ganin an samarwa masu dauke da cutar magani.

Ana gudanar da bikin ranar yaki da cutar kanjamau ne kowacce ranar 1 ga watan Disamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.