Najeriya-Ta'addanci

An samu raguwar aikata ayyukan ta'addanci a Najeriya cikin 2019- rahoto

Wasu jami'an Sojin Najeriya da ke yaki da ta'addanci.
Wasu jami'an Sojin Najeriya da ke yaki da ta'addanci. Reuters

Wani sabon rahoton hukumar da ke tattara alkaluman ta’addanci na Duniya GTI ta bayyana yadda aka samu raguwar ayyukan ta’addanci a sassan Najeriya cikin shekarar da ta gabata ta 2019, shekarar da rahoton ke bayyanawa da mafi karancin samun ayyukan ta’addanci da Najeriya ta gani cikin shekaru 8 da suka gabata.

Talla

Rahoton kungiyar ta GTI da ke fita a yau Laraba, ya nuna cewa alkaluman ayyukan ta’addancin ya sakko daga kashi 39 da Najeriya ke gani kowacce shekara tun daga 2011 zuwa kashi 27 a 2019 inda aka samu afkuwar ayyukan ta’addanci dubu 1 da 245.

Cikin rahoton GTI kungiyar da ke sanya idanu kan ayyukan ta’addanci a Duniya ta ce a shekarar 2018 hare-haren ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane ya hallaka mutane fiye da yadda hare haren Boko Haram ya yi.

Rahoton ya bayyana cewa raguwar ayyukan ta’addancin na da nasaba da raguwar hare-hare kan Fulani makiyaya da suka tsananta shekaru 2 zuwa 3 da suka gabata.

Rahoton na GTI a bana ya ce yanzu Najeriyar ce ta 6 a jerin kasashen da ke fama da ayyukan ta’addanci sabanin ta 3 da ta ke tun a shekarar 2015.

Yanzu haka dai Afghanistan ce ta daya a jerin kasashen da suka fi fuskantar ayyukan ta’addanci kana Iraq tukuna Syria sai Somalia da kuma Yemen sannan Najeriyar.

Sauran kasashen sun hada da Pakistan a matsayin ta 7 sannan India a matsayin ta 8 sai Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo a matsayin 9 kana Philippines a matsayin ta 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.