Bakonmu a Yau

Tattaunawa da Kakakin kungiyar ACF Emmanuel Yawe kan tabarbarewar tsaro a Arewacin Najeriya

Sauti 04:14
Gawarwakin wasu da 'yan Bidiga suka hallaka a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya.
Gawarwakin wasu da 'yan Bidiga suka hallaka a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya. thenationonlineng

Kungiyar ACF ta 'yan Arewacin Najeriya ta bayyana cewar harkokin tsaro a yankin sun tabarbare tun bayan taron da suka yi a watan Oktoba inda suka bukaci shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya sake damara.Sanarwar da mai Magana da yawun kungiyar Emmanuel Yawe ya rabawa manema labarai, ta bukaci shugaban kasar da ya tuna rantsuwar da ya yi da Alkur’ani mai girma cewar zai kare rayukan kowanne dan kasa.Dangane da wannan sanarwa Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da kakakin kungiyar kuma ga yadda zantawar su ta gudana.