Najeriya

Ya kamata APC ta mutunta tsarin karba-karba- Fashola

Babatunde Raji Fashola
Babatunde Raji Fashola REUTERS/Akintunde Akinleye

Ministan Ayyuka da Gidaje na Najeriya Babatunde Raji Fashola ya bukaci jam’iyyar APC mai mulkin kasar da ta mutunta tsarin karba-karba wajen tsayar da mutumin da zai yi mata takara a zaben shugaban kasa na 2023.

Talla

Fashola ya bayyana wannan tsarin na karba-karba a matsayin wata babbar yarjejeniya da iyayen da suka kafa APC suka cimma matsaya a kanta tun gabanin zaben 2015.

Fashola wanda lauya ne, ya rike mukamin gwamnan jihar Lagos lokacin da aka kafa APC, kuma ya kasance jigo a jerin masu ruwa da tsaki a jam’iyyar a wancan lokaci.

Tsokacin Fashola na zuwa ne a yayin da ake takaddama kan ko mulkin Najeriya zai koma yankin Kudancin kasar da zarar shugaba Muhammadu Buhari ya kammala wa’adinsa na biyu a 2023.

Gwamnan Ebonyi David Umahi ya sauya sheka daga PDP zuwa APC saboda irin wannan takadda kan tsarin karba-karba tsakanin shiyoyin kasar.

Gwamnan ya ce, ya sauya sheka ne saboda PDP ba ta taba tsayar da dan takarar shugaban kasa daga yankin Kudu maso gabashin kasar ba tun bayan da aka koma mulkin farar hula a 1999.

Har ila yau, jiga-jigan APC karkashin shugabanta na riko kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni sun ziyarci tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, matakin da ya haifar da rade-radin cewa, jam’iyyar mai mulki na zawarcin sa don ganin ya sauya sheka daga PDP zuwa APC, sannan ta tsayar da shi a matsayin dan takararta a 2023.

Wasu na cewa, APC na son shawo kan Jonathan ne ganin cewa, ba zai wuce ya yi wa’adi daya ba kan karaga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.