Maiduguri

Mu dauki matakan hana matsalar satar mutane zuwa yankin mu - Zulum

Gwamnan jihar Barno Babagana Umara Zulum yayin taron kungiyar gwamnonin arewa maso gabashin kasar da ya jagoranta a Yola na jihar Adamawa
Gwamnan jihar Barno Babagana Umara Zulum yayin taron kungiyar gwamnonin arewa maso gabashin kasar da ya jagoranta a Yola na jihar Adamawa RFI Hausa

Gwamnan Jihar Barno da ke arewa maso gabshin Najeriya, Farfesa Babagaba Umara Zulum ya ce, ya zama dole su kara azama domin ganin an dauki matakan da suka dace wajen ganin matsalar masu garkuwa da mutane da ake bi har gida bai yadu zuwa yankin arewa maso gabashin kasar ba.

Talla

Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne yayin taron Kungiyar gwamnonin yankin arewa maso gabashin Najeriya karo na uku da ya jagoranta, a Jimeta dake birnin Yola na Jihar Adamawa.

Farfesa Babagana Zulum ya ce ganin yadda wannan matsala ta satar mutane ana garkuwa da su domin karban kudin fansa ke kara ta'azzara a kasar, masamman a johohi irinsu Kano da Kaduna, da Zamfara da sauransu, akwai bukatar kungiyar tasu ta dauki kwararan matakai don dakile isar haka zuwa yankin nasu.

Gwamnan yace, yankin arewa maso gabashin kasar, yanzu haka na fama da matsololin tsaro dake alaka da mayakan Boko Haram, bai kamata suyi sake matsalar garkuwa da mutane ya riske su, inda ya jinjinawa rundunar tsaron kasar a kokarin da sukeyi ba dare ba rana don kawo karshen matsalar da yanzu ya rage a dajin Sambisa da yankin tafkin Chadi.

Shugaban gwamnonin na yankin ya kara da cewa, hakan bazai samu ba, sai an dauki matakan inganta rayuwar al’umma, wajen samar wa matasa ayyukanyi da kuma kawo karshen almajiranci dake gararamba a titina.

Taron wanda ya samu halartan gwamnonin Bauchi da Gombe da mai karban bako na Adamawa sai kuma mataimakan gwamnonin Taraba da Yobe, ya kuma tattauna batutuwa da suka shafi matsalar fyade, da lalubo hanyar kare mata tare da basu karfin gwiwar rayuwa kamar kowa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.