Najeriya

Yaran Kano za su fara karatu kyauta kuma dole

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Kano State Government

Gwamnan jihar Kano da ke Najeriya Abdullahi Umar Ganduje ya sanya hannu kan dokar bada ilimi kyauta kuma dole tun daga matakin firamare har zuwa sakandare a jihar.

Talla

Sanya hannu kan wannan doka na nufin cewa, daga yanzu ya zama wajibi ga iyaye su sanya ‘ya'yansu a makarantar boko musamman wadanda suka kai munzalin fara karatu

A lokacin da yake rattaba hannu kan dokar, Ganduje ya ce akwai hukunci mai tsanani ga duk iyayen da suka karya dokar ta 'karatu dole' a duk fadin jihar ta Kano.

Wata kididdigar baya-bayan nan da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar ta nuna cewa, jihar Kano ce ke da adadi mafi yawa na yaran da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, inda adadinsu ya doshi miliyan guda da rabi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.