Najeriya

Ana gaf da kawo karshen yajin aikin jami'o'i a Najeriya

Daliban jami'a a Najeriya
Daliban jami'a a Najeriya The Guardian Nigeria

RahotanniI daga Najeriya na nuna cewar ana gaf da janye yajin aikin da malaman jami’oi suka kwashe watanni suna yi, sakamakon tattaunawar da bangarorin suka yi wadda ta kaiga kulla yarjejeniya.

Talla

Bayan taron da suka gudanar juma’ar nan, gwamnati ta amince ta biya malaman naira biliyan 40 a matsayin kudaden daunin su da kuma bada wasu naira biliyan 30 domin inganta makarantun, tare da biyan albashin watan Fabarairu zuwa Yuni nan da ranar 31 ga watan Disamba.

Gwamnatin ta kuma amince ta cire malaman daga cikin tsarin biyan albashin ta na bai daya da ake kira IPPIS wanda ya gamu da mummar suka daga malaman da masu sanya ido kan yadda ake tafiyar da jami’oi.

Ministan kwadago Chris Ngige ya tabbatar da matakan da aka dauka, wanda zai baiwa shugabannin malaman komawa domin gabatar da su ga mambobin su.

Shugaban kungiyar malaman Farfesa Biodun Ogunyemi ya tabbatar da matsayin gwamnatin ba tare da Karin haske akai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.