Maiduguri

Boko Haram ta yiwa Manoma 43 yankan rago a Barno

Wani motar da mayakan Boko Haram sukayi amfani da shi wajen kai hare hare
Wani motar da mayakan Boko Haram sukayi amfani da shi wajen kai hare hare AUDU MARTE / AFP

Rahotanni daga Jihar Barno dake arewa maso gabashin Najeriya sun ce mayakan Boko Haram sun kashe manoma 43 da kuma jikkata wasu 6 lokacin da suke aiki a gonakin shinkafa kusa da birnin Maiduguri.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa yace mayakan sun daure manoman ne kafin suyi musu yankan rago a kauyen Koshobe.

Babakura Kolo, shugaban kungiyar sa kai da ya taimakawa wadanda suka tsira daga harin, yace sun kwaso gawarwaki 43 da aka yanka tare da wadanda suka samu raunukan.

Wani dan kungiyar sa kan Ibrahim Liman ya bayyana wadanda aka kashe a matsayin leburorin dake aiki a gonar da aka dauko hayar su daga Jihar Sokoto.

Liman yace leburorin su 60 aka dauki hayar su domin girbe shinkafar, kuma daga cikin su aka yanka 43, yayin da 8 daga cikin su suka bata.

Ko a watan jiya kungiyar Boko Haram ta kashe manoma 22 dake aikin noman rani Zabarmari dake kusa da birnin Maiduguri.

Rikicin Boko Haram ya yi sanadiyar kashe mutane akalla 36,000 tun bayan barkewar sa a shekarar 2009, yayin da yaraba mutane sama da miliyan 2 daga muhallin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.