Najeriya

Zulum ya jagoranci jana'izar manoman da Boko Haram ta kashe

Gwamnan jihar Barno Babagana Umara Zulum yayin jana'izar manoma 43 da Boko Haram ta kashe a jihar
Gwamnan jihar Barno Babagana Umara Zulum yayin jana'izar manoma 43 da Boko Haram ta kashe a jihar RFI Hausa

Gwamnan Jihar Barno da ke Najeriya Babagana Umara Zulum ya jagoranci jana’izar manoma 43 da mayakan Boko Haram suka yi wa yankan rago a Kashobe da ke jihar j

Talla

Daruruwan mutane ne suka halarci janaizar cikinsu har da tawagar gwamnan da kuma jami’an tsaro, yayin da wani mazaunin garin ya shaida masa cewar, bayan wadannan gawarwaki 43, akwai wasu mutane da suka bata wadanda ba san halin da suke ciki ba.

Gwamna Zulum ya mika sakon ta’aziyarsa ga mazauna garin, inda ya shaida musu cewa, sun kwashe daren jiya suna tattauna matsalar tare da hafsoshin tsaro da zummar ganin an gano wadanda suka bata.

Zulum ya bayyana cewar mutanensa na cikin tsaka mai wuya dangane da halin da ake ciki a jihar, inda ake kai musu hari a wajen gidajensu, kuma idan sun zauna a gida ma, ba su tsira ba.

Gwamnan ya sake kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki karin matasan yankin daga cikin 'Yan sa kai da mafarauta domin sanya su aikin soji da jami’an tsaron farin kaya domin kare manoman.

Zulum ya ce suna bukatar karin jami’an tsaro domin kare manoman, kuma matasan yankin sun fahimci yanayin wurin da za su iya bada gudummawa.

Kuna iya latsa alamar sauti dake kasa don sauraron rahoto akai.

Rahoto kan yadda aka gudanar da zana'izar manoman da Boko Haram ta kashe a Barno

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.