Bakonmu a Yau

Farfesa Mohammed Kabir Isa kan kissan manuma sama da 100 da Boko Haram ta yi a Barno

Sauti 03:29
Gwamnan jihar Barno Babagana Umara Zulum yayin jana'izar manoma 43 da Boko Haram ta kashe a jihar
Gwamnan jihar Barno Babagana Umara Zulum yayin jana'izar manoma 43 da Boko Haram ta kashe a jihar RFI Hausa

Alummar jihar Borno dake arewa maso Gabashin Najeriya na cikin zaman makoki yanzu haka sakamakon kazamin harin da mayakan Boko Haram suka kai tare da kashe sama da mutane 100 kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta sanar, akasarinsu manuma shinkafa. 

Talla

Wannan ya kasance mafi muni a cikin hare-haren da mayakan kungioyar Boko Haram ke kaiwa duk da matakan da Gwamnatin kasar ke cewa ta na dauka.

Dangane da haka, Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Farfesa Mohammed Kabir Isa na Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria, wanda ke bincike dangane da ayyukan Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.