Boko Haram-Najeriya

Sojojin Najeriya sun yi watsi da adadin Majalisar Dinkin Duniya

Gwamnan jihar Barno Babagana Umara Zulum yayin jana'izar manoma 43 da Boko Haram ta kashe a jihar
Gwamnan jihar Barno Babagana Umara Zulum yayin jana'izar manoma 43 da Boko Haram ta kashe a jihar RFI Hausa

Ma'aikatar Tsaron Najeriya ta yi watsi da adadin manoman da mayakan Boko Haram suka kashe a jihar Barno, wanda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar sun kai 110.

Talla

Jami’in yada labaran ma’aikatar tsaron Manjo Janar John Enenche yace mutane 43 aka yanka sabanin 110 da rahotan Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana.

Janar Enenche yace har ya zuwa safiyar wannan Litinin babu Karin adadin da aka samu daga mutane 43 da akayi janaizar su ranar Lahadi a Zabarmari, domin jami’an sojojin dake wurin sun kidaya wadanda aka kashe tare da mazauna yankin.

Jami’in yace har zuwa daren Lahadi yana tintibar kwamandodin su dake aiki a Jihar Barno dangane da abinda ya faru da kuma halin da ake ciki, amma babu wanda ya bada adadin da suka zarce 43.

Janar Enenche yace wata kila adadin na iya tashi nan gaba amma ba gaskiya bane adadin 110 da Majalisar ta bayar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.