Najeriya-Boko Haram

'Yan gudun hijira dubu 3 sun koma gida bayan kisan manoma 110 a Maiduguri

Wasu 'yan gudun hijira a yankin Muna Garage da ke birnin Maiduguri na jihar Borno a Najeriya.
Wasu 'yan gudun hijira a yankin Muna Garage da ke birnin Maiduguri na jihar Borno a Najeriya. REUTERS/Paul Carsten

Rahotanni daga Jihar Borno a Arewacin Najeriya na cewa an fara aikin mayar da wasu ‘yan gudun hijira kimanin dubu 3 matsugunansu bayan da rikicin ya tilasta musu tserewa daga muhallansu shekaru 6 da suka gabata.

Talla

Shirin mayar da ‘yan gudun hijirar na zuwa bayan wani farmakin Boko Haram da ya hallaka manoman shinkafa 110, adadi mafi yawa da harin ta’addanci ya hallaka lokaci guda a shekarar nan.

‘Yan gudun hijirar wadanda galibinsu suka fito daga yankin Marte a yankin tafkin Chadi bayanan na nuna cewa sun bar gidajensu ne tun cikin shekarar 2014 bayan tsanantar hare-haren ta’addanci da Boko Haram ke kaddamarwa a yankin arewa maso gabashin Najeriyar.

Wasu ganau a aikin mayar da gudun hijirar muhallansu sun ce anyi amfani da manyan motocin safa wajen kwashe ‘yan gudun hijirar daga sansaninsu da ke tsakiyar birnin Maiduguri.

Sanarwar hukumar agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta ce an tanadi dukkannin abin bukata ga ‘yan ciranin wadanda aka fara aikin mayar da su muhallan na su a yau Litinin.

Mai magana da yawun hukumar Abdulkadir Ibrahim ya ce akalla magidanta 500 ke cikin jumullar masu komawa gidajen nasu dubu 3 da hukumar ta zabo daga sansanonin ‘yan gudun hijira 4 da ke cikin birnin na Maiduguri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.