Najeriya

Najeriya ta kamo tsohon shugaban kwamitin fanshonta da ya gujewa kotu zuwa Nijar

Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban kwamitin Fansho da EFCC ke tuhuma da karkatar da kudin da yawansu ya haura biliyan 2.
Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban kwamitin Fansho da EFCC ke tuhuma da karkatar da kudin da yawansu ya haura biliyan 2. facebook/EFCC

Hukumomin tsaron Najeriya sun yi nasarar kama Abdurasheed Maina, tsohon shugaban kwamitin fansho da Hukumar EFCC ke tuhuma da bacewar akalla naira biliyan 2 a karkashin sa.

Talla

Wasu kafofin yada labaran kasar da suka hada da PR Nigeria da ake wallafawa sun ce jami’an liken asirin Najeriya da na Hukumar EFCC sun yi nasarar kama Maina ne a Jamhuriyar Nijar a karkashin yarjejeniyar aiki tare da kasashen biyu suka sanya hannu akai.

Kotu ta bada belin Maina bayan gindaya sharudda masu tsauri cikinsu harda gabatar da mai rike da mukamin Sanata, abinda ya sa Sanata Ali Ndume daga Jihar Borno ya gabatar da kan sa, a matsayin wanda ya fito daga yankinsa, amma kuma daga bisani aka neme shi aka rasa.

Wannan ya sa alkalin kotun bada umurnin tsare Sanata Ndume da kuma kwace gidan sa da ya gabatar a matsayin kadarorin karbar beli.

Bayan kwashe kwanaki a gidan yarin Kuje da ke Abuja, kotun ta bada belin Sanata Ndume wanda ya bayyana halin da ya shiga a matsayin kaddara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.