Najeriya

An gano karin manoma da mayakan Boko Haram suka kashe a Borno

Yadda aka yi jana'izarmanoman da mayakan Boko Haram suka yiwa kisan gilla ta hanyar yankan rago a garin Zabarmari dake jihar Borno. 29/11/2020.
Yadda aka yi jana'izarmanoman da mayakan Boko Haram suka yiwa kisan gilla ta hanyar yankan rago a garin Zabarmari dake jihar Borno. 29/11/2020. REUTERS/Ahmed Kingimi

Gwamnatin jihar Borno da ke Najeriya ta ce adadin manoman da mayakan Boko Haram suka kashe a baya bayan nan na karuwa, sakamakon ci gaba da gudanar da bincike da ake yi.

Talla

Yayin zantawa da sashin Hausa na RFI, Kwamishinan yada labaran jihar Baba Kura Abbajato ya ce a halin yanzu adadin manoman da aka gano mayakan na Boko Haram sun yiwa kisan gilla ya kai 81.

Kwamishinan ya kuma kara da cewa akalla mutane 111 ne ke gonar a yayinda kungiyar ta Boko Haram ta kai mummunan farmakin.

Kwamishinan yada labaran Borno Baba Kura Abbajato kan gano karin gawarwakin manoman da mayakan Boko Haram suka halaka

Kafin sanarwar da gwamnatin Borno ta fitar a baya bayan nan, an yi ta samun rahotanni masu cin karo da juna dangane da adadin manoman da suka rasa rayukansu a harin na Boko Haram, inda da fari gwamnatin Najeriya ta ce 43, yayinda majalisar dinkin duniya ta ce adadin ya kai 110, kafin janye rahoton daga bisani.

Tuni dai shugaban kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau ya tabbatar da cewar mayakansa ne suka kashe manoman shinkafa 78 a Kwashabe da ke Karamar Hukumar Jere ta Jihar Borno.

A wani faifan bidiyo na minti 3 da ya fitar, Shekau ya tabbatar da kisan wanda ya bayyana a matsayin ramuwar gayya sakamakon kashe wani dan uwansu da kuma mika wani ga sojojin Najeriya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.