An yi min tsirara saboda Buhari-Naja'atu Muhammed
Wallafawa ranar:
A yayin da al'ummar Najeriya ke ci gaba da bayyana damuwa kan tabarbarewar tsaro a kasar, daya daga cikin mutanen da suka yi tsayin-daka don ganin jam'iyyar APC ta karbe mulki daga hannun PDP a 2015, wato Hajiya Naja'atu Muhammad ta ce, gwamnatin Buhari ba ta tausayin talakawa, sannan ta gaza wajen kare rayukansu da dukiyoyinsu. Naja'atu ta kuma bayyana irin mummunan halin da ta shiga saboda Buhari, tana mai cewa, an yi mata tsirara tare da dirka mata guba saboda shi amma ya gaza biyan al'ummar kasar.
Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar da Muhammad Sani Abubakar ya yi da Hajiya Naja'atu Muhammed.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu