Jami’an tsaron Najeriya sun karbi Maina daga takwarorinsu na Nijar
Wallafawa ranar:
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta maida AbduRasheed Maina tsohon shugaban kwamitin kula da kudaden fanshon kasar gida, bayan karbo shi daga hannun jami’an tsaron Jamhuriyar Nijar da suka kama shi a ranar Talatar da ta gabata.
Sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya Frank Mba a yau ce ta sanar da samun nasarar sake kame Maina da jami’an tsaron Najeriyar suka yi.
Jami’an tsaron Nijar sun cafke Maina ne bayan shelar neman sa ruwa a jallo tare da bada sammacin kamo shi da babbar kotun Najeriya ta yi, dangane da jerin tuhume-tuhumen da yake fuskanta kan almundahanar makudan kudaden fansho.
A watan Satumban shekarar 2019 Maina ya daina halartar zaman kotu, bayan bada shi beli yayin da yake fuskantar tuhume-tuhume 12 kan halasta kudaden haramun na fansho da yawansu ya kai naira biliyan 2.
Wannan ce ta sanya babbar kotun Najeriya ta bada umarnin tsare Sanata Ali Ndume da a baya ya tsayawa Maina kafin bada shi Beli, sai dai bayan shafe wasu ‘yan kwanaki a tsare, kotun ta bada belin Sanatan a ranar Juma’ar da ta gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu