Najeriya

Mai yiwuwa Najeriya ta cigaba da fuskantar ta’addanci nan da shekaru 20 - Buratai

Laftanar Janar Tukur Buratai, shugaban rundunar sojin Najeriya.
Laftanar Janar Tukur Buratai, shugaban rundunar sojin Najeriya. AFP / PIUS UTOMI EKPEI

Shugaban Rundunar Sojin Najeriya Janar Yusuf Tukur Buratai yace akwai alamun cewar ayyukan ta’addanci na iya daukar shekaru 20 ana fama da shi a kasar.

Talla

Buratai yace daukar matakin bai daya da ya shafi hadin kai tsakanin soji da fararen hula zai taimaka gaya wajen shawo kan matsalar.

Kalaman babban hafsan rundunar sojin Najeriyar dai ya haifar da karin cece-kuce kan muhawarar da ake tafkawa kan halin da tsaro ke ciki a kasar, biyo bayan kisan gillar da mayakan Boko Haram suka yi wa sama da manoma 70 a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, da kuma hare-haren ‘yan bindiga da yin garkuwa da mutane dake cigaba da karuwa a arewa maso yammacin Najeriyar.

A baya bayan nan ne dai gwamnonin jihohin dake arewa maso gabashin Najeriya suka goyi bayan kiraye-kirayen da ake yi wa gwamnatin tarayyar kasar na dauko sojojin haya domin murkushe mayakan Boko Haram da suka addabi yankinsu.

Gwamnan jihar Taraba darius Ishaku ne ya bayyana matsayin gwamnonin arewa maso gabashin Najeriyar a ranar talata, lokacin da suka ziyarci takwaransu na Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, don jajanta kisan gillar da mayakan Boko Haram suka yi wa manoma da dama a karamar hukumar Jere.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.