Najeriya

Sarkin Musulmi ya nuna damuwa kan halin da tsaro ya shiga a Najeriya

Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III.
Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III. YouTube

A Najeriya mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na III ya bayyana damuwa kan yadda ‘yan bindiga ke rike da ikon yankuna da dama a kasar, bayan hare-haren baya-bayan nan ciki har da Zabarmari da Boko Haram ta hallaka manoman shinkafa.

Talla

Cikin kalaman Sarkin na Musulmi wanda ke kunshe a wata sanarwa da kungiyar Jama'atu Nasrul Islam ta fitar ya ce, yanzu haka ‘yan bindigan na shinfida wa al’umma wasu ka’idojin da suka zama dole su mutuntasu kafin basu damar ci gaba da al'amuransu na yau da kullum.

Al'amuran tsaro na ci gaba da tabarbarewa a Najeriyar musamman yankin Arewaci inda ko a farkon makon nan mayakan kungiyar Boko Haram da ke biyayya ga IS wato ISWAP suka sace wani ma’aikacin jin-kai da wasu jami’ai biyu a arewa maso gabashin kasar.

Rahotanni sun ce an sace mutanen ne a wani shingen ababen hawa da ke kauyen Wakilti na jihar Borno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.