Bakonmu a Yau

Tattaunawa da Sheikh Sani Yahya Jingir kan matsalolin tsaro a arewacin Najeriya

Sauti 04:05
shugaban Malam kungiyar Izala, Sheikh Sani Yahya Jingir
shugaban Malam kungiyar Izala, Sheikh Sani Yahya Jingir Daily Trust

‘Yan Najeriya na cigaba da bayyana ra’ayoyi daban daban dangane da matsalar tsaro musamman a yankin arewacin kasar, bayan kazamin harin da aka kai jihar Barno wanda yayi sanadiyar yanka manoma 78.

Talla

Kungiyoyin 'yan arewacin kasar da gwamnoni da malaman Addini na cigaba da kira ga gwamnati da ta sake kara himma domin kare jama’a, yayin da majalisun kasar suka bukaci shugaban kasa yayi musu bayani kan halin da ake ciki.

Shi ma dai Mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa’ad Abubakar ya koka kan halin da jama’a ke ciki a yankin. Kan wannan al'amari ne muka tattauna da shugaban Malam kungiyar Izala, Sheikh Sani Yahya Jingir.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.