Jami'ar Amurka ta musanta karrama Ganduje da aikin malanta

Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano a Najeriya.
Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano a Najeriya. africatodaynewsonline

Wata jami’ar Amurka ta musanta rahotonnin da ke cewa ta baiwa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar

Talla

Jami’ar East Carolina University (ECU) ta ce wasikar da Ganduje ya samu ba da yawunta aka rubuta ta ba, hasali ma wanda ya aike da ita bai nemi yardarta a hukumance ba.

Jami’ar ta bayyana matsayinta a game da wannan batu ne a wata wasika da ta aike wa gwamnan kuma ta tura wa jaridar Premium Times.

Tun da farko jaridar Premium Times ta ruwaito cewa kakakin Ganduje, Abba Anwar, ya shaida wa manema labarai cewa wani mai suna Victor Mbarika ne ya aike wa da gwamnan wasikar da ke kunshe da bayanin cewa an dauke a matsayin babban malami na wucin gadi a jami’ar.

Jami’ar ta tabbatar da cewa Mr Mbarika ma’aikacinta ne, amma kuma ta ce ba shi da izinin bayar da aiki makamancin wannan.

Wasikar da aka aike wa da gwamnan tun da farko ta ce an zabi a karrama shi da aikin ne saboda ingantaccen jagorancinsa da kuma inganta rayuwan al’umma da yake yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.