Najeriya

Zabukan cike gurbi: APC ta lashe Imo, Filato da Legas

Takardar kada kuri'a a zabukan Najeriya.
Takardar kada kuri'a a zabukan Najeriya. Reuters

Rahotanni daga Najeriya sun ce an samu karancin fitar masu kada kuri’a, yayin gudanar zabukan cike gurbi a jihohi 8 daga 11 a jiya asabar.

Talla

Daga cikin jihohin da kididdiga ta nuna karancin fitar akwai Kogi, Cross River, Borno, Imo, Katina da kuma Legas. Yayin da kuma a jihohi kamar Bauchi Da Zamfara adadin mutanen da suka fita zabukan cike gurbin ke da dama.

Wadanda suka sa ido kan gudanar zabukan dai sun bayyana rashin damuwa da zabuka, da kuma matsalolin na’urorin Card reader a matsayin wasu daga cikin dalilan da suka janyo karancin fitar jama’a a wasu wuraren.

Tuni dai sakamakon zabukan cike gurbin suka soma bayyana inda a Legas dan takarar APC Tokunbo Abiru ya lashe kujerar Sanata mai wakiltar gabashin Jihar inda ya doke abokin hamayyarsa Babatunde Gbodomasi na PDP.

A jihar Imo haka abin yake inda hukumar zabe ta sanar da nasarar dan takarar jam’iyyar APC Hakeem Adikun da ya lashe kujerar Sanata mai wakiltar arewacin jihar da kuri’u dubu 36 da 811, inda dan takarar jam’iyyar PDP Emmanuel Okewulonu ya zo na 2 da kuri’u, dubu 31 da 903.

A Filato hukumar zabe ta bayyana Farfesa Nora Dadut ta jam’iyyar APC a matsayin wanda ta lashe zaben cike gurbin kujerar sanata mai wakiltar yankin Filato ta Kudu.

Farfesa Daduut ta lashe zaben ne bayan samun kuri’u dubu 83 da 151, inda ta doke George Daika na PDP da ya samu kuri’u dubu 70 da 838.

An gudanar da zaben cike gurbin na yankin Filato ta Kudu ne, sakamakon mutuwar Ignatius Longjan dan majalisar dattijan da a baya ke wakiltar yankin.

Sai dai a jihar Zamfara, zaben cike gurbin kujerar dan majalisar jiha mai wakiltar Bakura bai kammala ba, kamar yadda hukumar zabe ta sanar, sakamakon aringizon kuri’un da aka gano a wasu rumfunan zabe 14.

Zuwa lokacin sanarwar dai, dan takarar jam’iyyar PDP Ibrahim Tudu ke kan gaba da kuri’u dubu 18 da 645, yayinda Bello Dankande Gamji na APC ke da kuri’u dubu 16 da 464.

A wani labarin kuma rundunar ‘yan sanda a Bayelsa ta sanar da dauko gawarwakin jami’anta 6, da hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da su, yayinda suke kan hanyar ta tsallaka ruwa zuwa yankin Okporoma da ke kudancin karamar hukumar Ijaw ta Kudu.

‘Yan sandan na kokarin zuwa karamar hukumar ce don samar da tsaro yayin gudanar da zaben cike gurbi na kujerar dan majalisar dattijai da ya gudana a ranar asabar, sai dai a daren ranar juma’a kwale-kwalen da suke ciki ya kife a ruwan da suke kokarin tsallakewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.