Najeriya-Maiduguri

Buhari ya zarta takwarorinsa na baya wajen inganta tsaro - Gwamnan Borno

Gwaman Jahar Borno Farfesa Baba Gana Umara zulum lokacin da ya sauka a jamhuriyar Nijar domin ziyarar 'yan gudun hijirar jihar sa
Gwaman Jahar Borno Farfesa Baba Gana Umara zulum lokacin da ya sauka a jamhuriyar Nijar domin ziyarar 'yan gudun hijirar jihar sa Borno Government

Gwamnan Jihar Barno da ke Najeriya Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce duk da kashe-kashen da ake samu a Jihar, shugaba Muhammadu Buhari ya fi shugabannin da suka gabace shi wajen inganta harkar tsaro a Jihar.

Talla

Yayin da ya ke jawabi ga Dattawan Arewacin Najeriya da suka ziyarce shi domin jajanta masa kan kazamin harin da ya hallaka manoma 78, Gwamnan ya ce alkaluman da suke da shi daga kananan hukumomi 27 na Jihar tun daga shekarar 2011 sun nuna cewar Buhari ya fi kokari wajen dakile hare-haren.

Gwamna Zulum ya ce sabanin a baya kafin lokacin Buhari da babu wanda ya isa ya shiga wasu yankunan Jihar, yanzu haka suna da mutane a sassa daban daban tare da Sarakunan su da suka koma gida da suka hada da Bama da Gwoza da Askira-Uba da Ngala da Monguno da Kukawa da damboa da Konduga da kuma Mafa.

Gwamnan ya ce sabanin wannan lokaci babu wanda ya isa ya ziyarci wadannan garuruwa ko kuma zama a cikin su, yayin da sarakunan su suka samu mafaka a wasu garuruwa.

Zulum ya ce matsalar tsaro a Jihar Barno kafin zuwan Buhari ta kai ga babu wanda zai iya barin birnin Maiduguri da nisa, abinda ya bai wa mayakan boko haram kwarin gwuiwar kai hari sansanin sojin da ke Monguno da Bama da Barikin Giwa da ke Maiduguri da kuma sansanin sojin hadin gwuiwa na kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ke Baga.

Gwamnan ya ce a wancan lokaci hare hare da tayar da bama bamai sun zama ruwan dare a sasasn birnin Maiduguri, amma zuwan Buhari ya dakatar da hakan, kuma kowa na iya ganin shaidar hakan.

Zulum ya ce yanayi ne na Dan Adam ya bayyana damuwa duk lokacin da aka samu matsala irin wannan, amma kuma idan an duba inda aka fito da halin da ake ciki yanzu, an samu cigaban tsaro fiye da yadda lamarin ya ke ada.

Tawagar kungiyar Dattawan Arewacin Najeriyar da ke karkashin jagorancin shugaban ta Audu Ogbeh da shugaba kwamitin amintattun ta Ambasada Shehu Malami sun jajantawa Gwamna Zulum da mutanen Borno kan wannan kisa tare da addu’oin samun zaman lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.