Najeriya

Jam'iyyar PDP ta goyi bayan shirin tsige Buhari daga mulki

Tambarin babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya.
Tambarin babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya. vanguardngr

Babbar Jam’iyyar adawa a Najeriya PDP ta kare matakin da 'ya'yanta suka dauka a zauren majalisar wakilai na kiran tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ta bukace su da su cigaba da Shirin.

Talla

Kakakin Jam’iyyar Kola Ologbodian ya ce bukatar tsige Buhari na daga cikin bukatun akasarin 'yan Najeriya a yau, kuma a matsayin su na Jam’iyya ko da yaushe suna bukatar 'yan Majalisun su da su dinga aiwatar da abin da jama’a ke bukata domin kare martabar kasar.

Jam’iyyar ta ce tuni gwamnatin Buhari ta amsa gazawa kamar yadda daya daga cikin jami’an ta ya bayyana, cewar kasar ta fada hannun 'yan bindiga da 'yan ta’adda, abinda ke nuna gazawar su wajen samar da mafita.

Sai dai kakakin Jam’iyyar APC Yekini Nabena ya yi watsi da wannan matsayi, wanda ya ce tuni Majalisa ta bayyana shi a matsayin yunkurin dakile shirin shugaban kasa na zuwa Majalisar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.