Bakonmu a Yau

Farfesa Garba Umar Danbatta kan gudunmawar bangaren sadarwa wajen dakile matsalolin tsaro

Sauti 04:05
Shugaban hukumar sadarwar Najeriya Farfesa Garba Umar Danbatta
Shugaban hukumar sadarwar Najeriya Farfesa Garba Umar Danbatta Daily Trust

A koda yaushe ‘Yan Najeriya na bayyana damuwa kan yadda mayakan Boko Haram da kuma masu garkuwa da mutane ke amfani da wayoyi wajen tuntubar jama’a ba tare an gano inda suke ba.Wannan matsala da ta haifar da koma baya a yankin arewacin kasar ta sa ana nuna yatsa kan hukumar sadarwa wadda ke da alhakin taimakawa wajen gano irin wadannan batagari.Dangane da wannan matsala Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da shugaban hukumar sadarwar kasar Farfesa Garba Umar Danbatta, kuma ga abinda ya shaida mana akai.