Najeriya-Katsina

'Yan sanda sun ceto dalibai sama da 200 daga hannun 'yan bindiga a Katsina

Harabar wani ofishin 'yan sanda a Najeriya
Harabar wani ofishin 'yan sanda a Najeriya AFP

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a Katsina ta sanar da ceto sama da daliban makarantar sakandaren kimiyya ta Kankara daga hannun ‘yan bindigar da suka yi awon gaba dasu bayan farmakin da suka kaiwa makarantar a daren jiya Juma’ar.

Talla

Sai dai rundunar ‘yan sandan ba ta bayyana adadin daliban da ‘yan bindigar suka sace ba.

Kafin sanarwar ‘yan sandan dai rahotanni sun cewa kimananin dalibai 600 ake farbagar ‘yan bindigar sun sace yayin farmakin da suka kaiwa makaranatar sakandaren kimiyyar ta Kankara, la’akari da rashin ganin daliban jim kadan bayan harin.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito wani malami da ya nemi sakaya sunansa na cewa ‘yan bindigar sun afkawa musu ne da misalin karfe 9:30 na daren jiya Juma’a.

Farmakin na baya bayan bayan na zuwa ne sa’o’I bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya soma hutun mako 1 a mahaifarsa ta Daura dake jihar ta Katsina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.