Najeriya

Najeriya ta kashe Naira miliyan 100 wajen sayen alkalami da tawada

Majalisar Dokokin Najeriya
Majalisar Dokokin Najeriya Daily Trust

Kwamitin Majalisar Dattijan Najeriya mai kula da yadda hukumomin gwamnati ke kashe kudaden al’umma, ya bayyana kaduwa kan rahoton binciken da ya bankado cewar wasu jami’an ma’aikatar kula da albarkatun man fetur sun kashe naira miliyan 116 wajen sayen alkalamin rubutu, takardu da kuma tauwada cikin shekara 1.

Talla

An gudanar da wannan bincike ne tun a shekarar 2015, wanda a yanzu haka Majalisar Dattijan Najeriya ke bibiyarsa.

Rahoton ya ce ma’aikatar kula da albarkatun man fetur din Najeriya ta kashe naira miliyan 14 da dubu 500 ne wajen sayen alkalamin rubutu na kamfanin Schneider, naira miliyan 46 wajen buga takardu masu dauke da hatimin ma’aikatar, sai kuma amfani da naira miliyan 56 wajen sayen tauwada da na’urorin sake bugun takardu duk cikin shekara guda.

Wannan dai bashi ne karo na farko da ake bankado irin wannan badakala a wasu hukumomi ko ma’aikatun Najeriya ba, domin kuwa a watan Agustan da ya gabata hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC a Najeriya, to soma bincikar manyan jami’an hukumar raya yankin Niger Delta NDDC, kan zarge-zargen halasta kudaden haramun da kuma sace makudan kudaden da gwamnati ta ware don yakar annobar coronavirus, da yawansu ya kai naira biliyan 5 da kusan rabi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.