Bakonmu a Yau

Tattaunawa da Malam Mustapha Masaudu dan uwa ga daya daga cikin daliban Katsina da 'yan bindiga suka sace

Sauti 03:36
Allon makarantar sakataren kimiyya da Kankara dake jihar Katsina
Allon makarantar sakataren kimiyya da Kankara dake jihar Katsina Daily Trust

Yayainda da ake cigaba da dakon ceto tarin daliban da 'yan bindiga suka sace a makarantar Sakandaren Kankara da ke Jihar Katsina, wasu mutane na bayyana tababa dangane da yaran da suka bata, duk da ya ke Gwamnan Jihar ya ce suna neman dalibai 333.Yanzu haka wasu iyayen yara na can sun yi dafifi a makarantar suna jiran alkawarin da ministan tsaro ya yi cewar nan bada dadewa ba za’a kubutar da su.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da wani da aka sace kaninsa, kuma yanzu haka suna can suna zaman dirshe a Kankara Malam Mustapha Masaudu, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.