Najeriya

Buhari na shan matsin lamba kan bukatar korar hafsoshin tsaron Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Nigeria Presidency/Handout / REUTERS

‘Yan Najeriya da suka hada da jama’ar gari, kungiyoyi da kuma fitattun mutane na cigaba da nanata kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya kori manyan hafsoshin rundunonin tsaron kasar, sakamakon yadda matsalar tsaro ke cigaba da yin muni.

Talla

Tsohon gwamnan Borno kuma Sanata mai wakiltar yankin tsakiyar jihar Kashim Shettima na daga cikin fitattun mutanen da a baya bayan nan suka nanata bukatar sallamar shugabannin rundunonin tsaron, la’akari da gazawarsu wajen magance matsalolin tsaron dake addabar sassan kasar.

Yayin wata zantawa da kafar talabijin ta Arise, Shettima yace kamata yayi shugaban Najeriya ya maye guraben manyan hafsoshin tsaron kasar ta mutane masu hikima da sabbin dabarun tunkarar kalubalen da fannin tsaro ke fuskanta gami da kawo karshensa.

A baya bayan nan nedai shi ma tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okoracha, ya shawarci shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari da ya kori dukkanin mukarrabansa.

A cewar Okorocha, gazawar da gwamnati mai ci ta yi wajen tsare rayuka da dukiyoyin al’umma ya fusata ‘yan Najeriya matuka, dan haka kamata ya yi shugaban kasar ya maye mukarrabansa na yanzu da wadanda za su sauke nauyin hakkin da za a dora musu.

Yanzu haka dai caccakar da shugaban Najeriya tare da manyan hafsoshin tsaronsa ke fuskanta na cigaba da karuwa, biyo bayan kisan gillar da mayakan Boko Haram suka yiwa manoma sama da 70 a yankin Zabarmari dake jihar Borno, sai kuma sace daruruwan daliban makarantar da ‘yan bindiga suka yi a garin Kankara dake jihar Katsina, harin da shima kungiyar ta Boko Haram ta yi ikirarin kaiwa a cewar jagoranta Abubakar Shekau.

A farkon watan disambar nan majalisar wakilan Najeriya ta kada kuri’ar amincewa da kudurin gayyatar shugaban kasar Muhammadu Buhari don yi mata bayani kan halin da sha’anin tsaro ke ciki, biyo bayan kisan gillar da mayakan Boko Haram suka yiwa manoman shinkafa a Zabarmari dake Borno.

Sai dai Ministan shari’ar Najeriya Abubakar Malami yace Majalisar dokokin kasar ba ta da hurumin gayyatar shugaba Buhari domin gurfana a gaban ta dangane da batun da ya shafi ayyukan soji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.