Najeriya

Jihohin arewacin Najeriya 3 sun yi umarnin sake kulle makarantu

Jihohin Kano Jigawa da Zamfara sun sanar da sake kulle makarantu
Jihohin Kano Jigawa da Zamfara sun sanar da sake kulle makarantu Twitter

Bayan sace daliban Sakandiren Gwamnati ta kankara 333 a jihar Katsina da ‘yan bindiga suka yi wanda daga bisani kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin hannu a ciki jihohin arewacin Najeriya 3 sun sanar da daukar matakin kulle makarantu.

Talla

Kwamishinan Lafiya na jihar Zamfara Ibrahim Gusau ya ce matakin kulle makarantun 10 da ke iyakar jihar da Katsina da kuma wadanda ke Iyaka da Kaduna na da nasaba da sake tabarbarewar al’amuran tsaro.

Ibrahim Gusau ya bayyana cewa makarantun da ke tsakiyar gari za su ci gaba da tafiyar da al’amuransu kamar yadda su ke.

Tun bayan matakin sace daliban Sakandiren a Katsina ranar 11 ga watan nan da muke ciki, hankula suka fara tashi kan makomar ilimi musamman a makarantun kwana, inda tun a wancan lokaci gwamnatin Katsina ta yi umarnin kulle ilahirin makarantun kwana.

Zuwa yanzu dai babu tabbacin ko kulle makarantun a jihohin Kano da Jigawa na da nasaba tsaro musamman la’akari da tsanantar cutar Covid-19 wadda zuwa yanzu aka samu sabbin kamuwa mutum 14 a jigawa.

Tun cikin daren jiya Talata ne gwamnatin Kanon ta bakin kwamishinan Ilimi na jihar Sanusi Kiru ya bayyana bukatar gaggauta kulle makarantun yayinda ya umarci iyaye yaran da ke makarantu kwana su gaggauta kwashe yaransu a yau Laraba.

Itama dai sanarwar kulle makarantun Jigawa ta bakin mukaddashin babban sakataren ma’aikatar ilmi Rabi’u Adamu ta umarci iyaye su gaggauta kwashe yaransu daga makarantun kwana a yau Larabab baya ga umartar makarantun jeka ka dawo su ci gaba da kasancewa a kulle.

Kusan watanni 3 kenan da makarantun suka sake budewa a sassan Najeriya musamman Arewacin kasar wadanda aka kulle su saboda tsanantar Coronavirus, duk da cewa hada-hadar bukukuwa, kasuwanni da kuma tarukan siyasa na ci gaba da gudana kamar yadda aka saba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.