Bakonmu a Yau

Tattaunawa da Hajiya Naja'atu Muhammad kan yadda cin hanci ya dabaibaye tsarin daukar sabbin 'Yansanda

Sauti 03:04
Naja'atu Bala Muhammad is a Nigerian politician, She is the first Kano state female politician to become a Senator, in Nigeria
Naja'atu Bala Muhammad is a Nigerian politician, She is the first Kano state female politician to become a Senator, in Nigeria RFI Hausa

Rahotanni daga Najeriya na nuna yadda matsalar cin hanci ta dabaibaye dibar 'yan Sandan da ya gudana a wannan shekara, inda ake zargin wasu jami’an hukumar da karbar makudan kudade suna sauya sunayen mataşan da suka samu nasara.Wannan matsala ta haifar da cece-kuce a cikin kasar, musamman a wannan lokaci da matsalar tsaro ta dabaibaye Najeriya baki daya.Muhammad Sani Abubakar ya tattauna da Haj Naja’atu Muhammad, kwamishiniya a Hukumar kula da aikin Yan Sanda dake Najeriya, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.