Najeriya

Buhari zai magance matsalolin tsaron da suka addabi Najeriya - Gwamnonin APC

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Twitter@BashirAhmaad

Gwamnonin jam’iyyar APC a Najeriya sun bayyana kwarin gwiwar cewa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai samu nasarar kawo karshen matsalolin tsaron dake addabar sassan kasar.

Talla

Gwamnonin na APC sun bayyana matsayin nasu ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabansu, kuma gwamnan jihar Kebbi Abubakar Bagudu, domin taya shugaban Najeriyar murnar cika shekaru 78, da suka fitar yau Alhamis a garin Abuja.

Har yanzu dai ‘yan Najeriya da suka hada da jama’ar gari, kungiyoyi da kuma fitattun mutane na cigaba da caccakar shugaba Muhammadu Buhari tare da bukatar ganin ya kori manyan hafsoshin rundunonin tsaron kasar, sakamakon yadda matsalar tsaro ke cigaba da yin muni.

Tsohon gwamnan Borno kuma Sanata mai wakiltar yankin tsakiyar jihar Kashim Shettima na daga cikin fitattun mutanen da a baya bayan nan suka nanata bukatar sallamar shugabannin rundunonin tsaron, la’akari da gazawarsu wajen magance matsalolin tsaron dake addabar sassan kasar.

Yayin wata zantawa da kafar talabijin ta Arise, Shettima yace kamata yayi shugaban Najeriya ya maye guraben manyan hafsoshin tsaron kasar da mutane masu hikima da sabbin dabarun tunkarar kalubalen da fannin tsaro ke fuskanta gami da kawo karshensa.

A baya bayan nan ne dai shi ma tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okoracha, ya shawarci Buhari da ya kori dukkanin mukarrabansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.