Najeriya

Hadarin Mota ya munana a Najeriya cikin watanni ukun karshen 2020

Kowacce shekara ana samun 'Yan Najeriya fin dubu 10 da hadurran mota ke kashewa a sassan kasar.
Kowacce shekara ana samun 'Yan Najeriya fin dubu 10 da hadurran mota ke kashewa a sassan kasar. Droits tiers.

Wasu alkaluman hukumar kiyaye afkuwar hadurra a Najeriya sun nuna yadda mutane dubu 1 da 76 suka rasa rayukansu a hadurran mota cikin watanni ukun karshen shekarar nan, hadurran da suka fi tsananta a Arewacin kasar wanda ake alakantawa da rashin hanyoyi masu kyau ko kuma tukin ganganci.

Talla

Alkaluman na FRSC kamar yadda kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya wallafa sun nuna yadda aka samu hadurra dubu 2 da 656 a sassan kasar.

Adadin na bana a cikin watanni ukun dai ya ninka na bara da aka samu hadurra 419 tare da salwantar rayuka 84 a makamancin lokacin.

Hukumar ta alakanta tukin ganganci da gudun wuce kima ko kuma rashin ingancin tayoyin mota a matsayin manyan dalilan da ke haddasa hadurran motar, ko da ya ke mutane na da yakinin yadda rashin ingancin titunan kasar musamman na Arewaci ke haddasa hadurran a mafiya yawan lokuta.

Wasu bayanai na nuna yadda hanyar Kano zuwa Kaduna zuwa Abuja ta zama babbar tushen salwantar rayuka saboda rashin inganci, bayan karuwar ayyukan ta’addanci musamman a wannna lokaci na bukukuwa da suka kunshi kirsimati da sabuwar shekara.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.