Tattaunawa da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle kan zargin da ake masa na daukar nauyin 'yan bindiga
Wallafawa ranar:
Sauti 03:04
Gwamnan Jihar Zamfara da ke Najeriya, Bello Mohamed Mutawalle ya musanta zargin da wasu ke yi masa na bai wa ‘yan bindiga damar cin karensu babu babbaka a jihar, ganin yadda ya ke yin sulhu da su da zummar magance matsalar sace jama’a da kashe-kashe.Gwamnan ya ce, a halin da ake ciki a yanzu, ba shi da wani zabi illa zaman tattaunawa da wadannan ‘yan bindiga , yana mai cewa, jami’an tsaron Najeriya ba su da isasshen kayan aiki na yaki da ‘yan ta’adda. Ga dai tattaunawar da gwamnan ya yi da abokin aikina Mohd. Sani Abubakar a Abuja.