Jaruma Aisha Gombi ta sha alwashin kara azama wajen yakar 'yan ta'adda a Najeriya

Sauti 03:33
Jaruma Aisha Bakari Gombi da ta shahara a fagen farauta da kuma yakar 'yan ta'adda a Najeriya.
Jaruma Aisha Bakari Gombi da ta shahara a fagen farauta da kuma yakar 'yan ta'adda a Najeriya. Twitter/@jeremyweate

Tun bayan rasuwar marigayi Ali Kwara Azare a Najeriya aka dain jin duriyar jaruman gargajiya dake tunkarar 'yan ta'adda dake addabar al'umma. Sai dai a baya bayan nan Jaruma Aisha Gombi dake jihar Adamawa tace ba barci suka yi ba, tare da shan alwashin bada tasu gudunmawar wajen kakkabe batagari daga cikin al'umma.Yayin ganawa da Gabra Aliyu Zaria, Aisha Gombi ta bukaci jama'a da su taimakawa jami'an tsaro da bayanai kan dukkanin wadanda basu aminta dasu ba.