Tattaunawa da Alhaji Mohammed Abba Kura kan yadda Kwastam ta kame kwantaina 133 dauke da miyagun kwayoyi a tashar jiragen ruwa ta Apapa

Sauti 03:31
Kwanturolan hukumar Kwastam shiyyar tashar jiragen ruwa na Apapa a Lagos Muhammad Abba-Kura.
Kwanturolan hukumar Kwastam shiyyar tashar jiragen ruwa na Apapa a Lagos Muhammad Abba-Kura. RFI Hausa / AbdoulKareem Ibrahim Shikal

Sashen hukumar yaki da fasa-kwauri na Najeriya da ke tashar jiragen ruwa na Apapa a jihar Lagos, ya sanar da kame kwantainoni 133 makare haramtattun magungunan asibiti ciki har da kwayar Tramol. A wani taron manema labarai da hukumar ta kira shugaban shiyyar Alhaji Mohammed Abba-Kura ya ce za su ci gaba da kara kaimi a yaki da ayyukan fasakwauri ta tashar ruwan. Ga dai yadda tattaunawarsu ta gudana da Garba Aliyu Zaria.